KUSKUREN DA WASU MUSULMI MASU RAUNIN IMANI WADANDA SUKA SHAGALA DA RAYUWAR DUNIYA SU KE YI A KALAMAN ADNAN OKTAR

Wadansu bangaren musulmi su kan dauki wani tsarin rayuwa na daban marar dadi wanda ya sha bamban da irin rayuwar da Alkur’ani ya nuna. Daya daga cikin kurakuran da irin wadannan mutane masu raunin imani da alfahari, wadanda ba su damu da aikin yada sakon musulunci ta hanyar dabi’u masu kyau ba, shi ne yadda suka dauki rayuwar wannan duniya kawai ba ta wuce mutum ya yi aure, ya haifi ‘ya’ya ya rene su sannan ya tara abin duniya ba. Tabbas wadannan abubuwa ne da ba su sabawa koyarwar musulunci ba. Amma inda kuskuren yake shine musulmi ya mance da babban dalilin zuwansa wannan duniya, wanda shine bauta da bin dokokin Allah, ya ta’allaka kawai kan aure da haifar ‘ya’ya, da kin tafiyar da ni’imomin da Allah ya yi masa akan tafarkin addini inda ya kan tafiyar da daukacin rayuwarsa cikin hanyar gulma da cin naman sauran musulmi alhalin ya watsar da kyawawan dabi’u na addini.

Adnan Oktar ya yi cikakken bayani a kan irin halayya da dabi’ar mutanen da suka yi kuskuren fahimtar tsarin musulunci a hirarraki da dama da a ka yi da shi inda ya kan yi kira ga al’ummar musulmi don su guji fadawa cikin irin wannan halayya marar kyau.


Babban dalilin samun rarraba a tsakanin musulmi a tsawon shekaru da kuma irin tashin hankali da zaluncin da a ke wa musulmi a sassan duniya daban daban, shi ne cewa wasu musulmin sun dauka rike sallah kadai da azumi da zuwa hajji sun ishe su addini, don haka ba ruwansu da al’amuran da ke da bukatar mika wuya da sadaukarwa domin ba abin da ya dame su kamar holewa da jin dadin rayuwar ni’ima da suke ciki, ba sa ko tunani game da matsalolin da ‘yan uwansu musulmi suke fuskanta a sassan duniya.

Misalin irin musulmi masu raunin imani da son kai, wadanda suke ruduwa da rayuwar duniya, suka yi watsi da kyawawan dabi’u na addini

“Babban burinsu shine su yi Aure Kuma su shiga kasuwanci”


“Akwai wasu mutane, kamar wadanda a ka bayyana, masu ra’ayin mazan-jiya ne koda yake suna da ra’ayin addini. Sun kasance suna aiki ko wani nau’i na kasuwanci ko sana’a. Suna da ‘ya’ya mata guda uku da kuma namiji guda daya. Shi dan ya na karatunsa a kasar waje, yayin da ‘yan matan kuma suke zaune a gida. Shin ka san ko me ‘ya’ya matan suke yi a gidan? Kawai a na jiran su girma ne a yi musu aure su ma su shiga haifar ‘ya’ya, iya manufar kenan ba su da wani buri. In ka tambayi mijin me ya sa a gaba, shine ya sami makudan kudi ya zama fitaccen dan kasuwa. “Wannnan shine buri na,” haka zai fada. “Me kuma ya rage banda wannan,” in ji shi. “In muka gaji da zama wuri daya, mu kan tafi Umra.” Ya kan rataye dardumar siliki mai hoton Ka’aba a bangon dakinsa, shi ke nan sai ya ci gaba da shekewarsa.” (An dauko daga hirar da Adnan Oktar ya yi da tashar talbijin ta Kanal 35 da Kanal Avrupa a ranar 31 ga Janairu, 2010.)


Musulmi mutane ne masu tsarkin zuciya da kyakkyawan tunani. Daya daga cikin halayen musulmi shine ba sa kallon sauran mutane ta mahangar jinsi ko al’ada, ko matsayin mutum a cikin al’umma ko kuma  kowane irin ma’aunin bambanci na duniya. Allah ne kadai ya san matsayin kowane mutum ta fuskar takawa, imani da kuma kusancinsa ga Allah mahalicci. Don haka Allah ya haramta wa muminai masu imani yin maganganu sabanin haka. Don mutumin da ya ce “Na yi imani” to ya zama lalle mu kyautata zato a gareshi tare da taimako da karfafarsa a duk lokacin da yake bukatar hakan.


“Sukan bayyana kansu a matsayin waliyai”

“Na sha ganin mutane suna tattauna darussan addini inda sukan dauki wani salon karya na daban don su nuna wa jama’a wai lalle suna da ruhin addini. Su kan daga kai suna duban sama, su yi tamkar suna tafiya ne a kan gajimare, ga kida kuma na tashi daga bayansu, suna riya wai su sufaye ne. Su kan yi wasu abubuwa da suka sabawa hankali, tare da kalamai a cikin wata irin murya da ba a iya gane abin da suke fada. Na sha ganin irin wadannan mutane da yawa. Ka ga suna wasu abubuwa kamar a irin wasan kwaikwayon sinima. In za ka tsaya ka kare musu kallo za ka ga dabi’arsu ta fita daban. Ko mutanen da suke nuna su waliyai ne; in suna magana sai su dinga daga kai sama don a ga kamar suna nazari ne. Da irin wannan halayya suke ambaton Annabinmu (saas) a maimakon su yi bayaninsa cikin hankali da hikima yadda kowa zai fahimta. Me ye ma amfanin hakan? Wa yace sai lalle sun yi wasu shu’umce shu’umce a cikin addini? Alkur’ani ya riga ya ba mu hujja, dama Alkur’ani shine tushen dalilai da hujja. Alkur’ani shine hujjarmu a duniya, kuma shine hujja ga dukkan mutanen duniya baki daya. Mutum mai hankali da basira shine wanda ke rayuwa a kan koyarwar Alkur’ani. Mutum mai hankali da wayo ya kan kara samun hikima idan ya rungumi koyarwar Alkur’ani. Tabbas basira ta kan samu da sannu sannu. Ba a haifar mutum da basira, sai dai ya kan same ta ne bayan zuwansa duniya. Haka nan shi ma hankali a kan sa wa mutum ne sannu a hankali, ma’ana babu wanda ke zuwa da hankalinsa cif a dunkule. Sannan sai batun yin kalamai da wasu harsunan waje, kamar latin ko larabci. Alal misali, mutanen turkiya ba sa jin harshen larabci, kuma kadan ne daga cikinsu su ke jin yaren. To don haka, me ya sa dole wai sai harshen larabci za a rika amfani da shi koda yaushe bayan ba kowa ne  ke jinsa ba? Kuma da ma mutanen suna fahimta to da babu laifi, hasali ma ba don mutane su koya a ke yin magana da yaren ba. To tun da ba da manufar koyarwa a ke yin sa ba, ka ga a na yi kawai don alfahari da nuna sani. Ka ji a na cewa “Kai, wannan mai ilimi ne.” Mu kan yi mu’amalarmu ta yau da kullum a cikin harshen Turkanci, cikin gwaninta da nakaltar harshen. Amma in za mu rika cakuda harsuna kamar mu rika cudanya Turkanci da karin furucin larabci abin zai zama bambarakwai. Ya kamata mu fahimci gaskiya. Misali, da turkanci mu kan ce “Ikhlas,” wato mutum da ke bauta tsakani da Allah da kyautata ibada, wannan shine abin da kalmar ta ke nufi a turkanci. Amma da an ji mun furta ta da “Ikhlas” mutane sai su ga kamar mun bata furucin kalmar ne, mun fada ba daidai ba. A haka ta ke a larabci, amma in a ka cudanya ta da turkanci sai ta bada wata ma’ana daban. In kuma mutum ya kasa furta kalmar daidai, to wannan kuma wani abu ne daban. Kuma rashin gaskiya ne mutum ya rika kokarin nuna shi mai ilimi ne ta hanyar kakale. Ya kamata mu yi abu da gaskiya ba don riya ba. Ba a ce dole sai mutum ya yi larabci kamar malamin Islamiyya ba. Kamar mutum yana alfahari ne da cewa “Na fi ku ilimi, ku zo in koya muku.”

Babu wanda ya san komai a cikinmu, Allah ne ya kimsa sani ga mutane kuma Shine ya ke kaddara furucinmu da kuma jin mu. Allah ne ya ke yin komai, mu tamkar kayan aiki ne a hannunSa. Mutane holoko ne. Ya zama wajibi mutum ya yi amfani da sassaukar hanyar sadarwa in yana so a fahimci sakonsa. Kuma hakan ya shafi lamarin fassarar Alkur’ani, in da ba a son rikitattun bayanai marasa kan gado da rudarwa. Duk wayo da fasahar mutum, in ya yi zancen shirme dole za a gane.” (An dauko daga hirar Adnan Oktar da tashar Kocaeli da Mavi Karadeniz ranar 26 ga Janairu, 2010.)

“Muminai maza da muminai mata mataimakan juna ne. Suna umarni da kyakkyawa kuma suna hani da mummuna, sannan suna tsaida sallah, da bada zakka kuma suna bin umarnin Allah da manzonSa. Wadannan Allah zai yi musu rahama. Allah mabuwayi ne, mai hikima.” (Sura Tauba, aya ta 71)

“Su kan gaskata duk sharri ko kazafi da a ka yi wa musulmi ba tare da bincike ba”

“Gaskata karairayin kage na ‘yan kungiyar asiri ta masons, da ‘yan kwaminis, ko karairayin ‘yan kungiyar Ergenekon, zai iya jawo wa musulmi wahala a ranar alkiyama. Duba ka ga yadda Allah mai girma ya ke cewa “Idan fasiki (wanda ba ya aiki da dokokin Allah) ya zo muku da labari, ku bincika.” Ku binciki gaskiyar labarin, don ku gani da idannunku, ku ji da kunnuwanku. Don kada ku yi saurin gaskata shi. Sai dai yanzu ba haka ne yake faruwa ba. A yau idan a ka buga labari a kan musulmi a cikin jarida ko mujallun makiya musulunci sai ka ji mutane na fadin “Kai, kai,  kai, ka ji abin da ke faruwa.” Suna zaune a gida sun harde kafafu suna kurbar shayi, ba sa wani kokarin taimakon addini banda holewa da jin dadin rayuwa, da shagalta da harkokin kasuwancinsu da kuma kula da jin dadin ‘ya’yansu tunda suna ganin ba wata matsala da ke damunsu a duniya. A daya bangaren kuma mutane ne da ke sadaukar da duk abin da suka mallaka a tafarkin Allah, kuma sun kasance suna gudun duniya Da shiga cikin hatsari, kuma su ne a ke wa sharri da kage, a ke zaluntarsu tare da wulakanta su. Duk da haka, sun kasance suna biyayya da gaskata wa ga wadancan nau’in mutane da ke kwance cikin gidajensu suna karanta labarai a jaridun makiya ‘yan kungiyar asiri. Babban abu kuma shi ne yadda a ka bar shi ya kare kansa da kansa. Sannan sauran mutanen can da babu ruwansu da addinin ko yada kiransa su ne za su zo suna yanke hukunci a kansa. Saboda haka sai su baro wa musulmi mai aikin yada addini sabon aiki; a maimakon shagalta da aikin addini, sai ya koma yana kokarin wanke kansa daga sharrin da suka dora masa. Alhali. Abin da ya kamata su wadancan cima-zaunen mutanen su yi shine su ce “Abokina, kyale ni in yi addini, bari in binciki gaskiyar labaran da fasikin nan yake yadawa, kar ka yi saurin gaskatawa. Zan yarda ne kawai da abin da idanuna ko kunnuwa na suka tabbatar mini cewa gaskiya ne.” Amma ba su yin haka. To, me rashin yin haka ya ke haifarwa? Ladan da musulmi zai samu zai ninka daga goma zuwa miliyan. Ka ga kenan wadancan masu kagen su ne dalilin samun ladan musulmi. Kuma wannan shine hikima a cikin halittar su, domin da babu mutumin da ke gaskata labarai daga wajen fasikai, da ladan da musulmi zai samu ya takaita. Su ne ke kara nauyin ladan musulmi, saboda haka halittarsu ma hikima ce babba. Ina fadin haka don mutane su san ainihin gaskiya don su san abin da za su tarar a ranar lahira. Ko ba  komai, ta wata fuskar su ma wadannan mutane suna da na su amfanin!” (An ciro daga hirar da Adnan Oktar   ya yi da tashar Adiyaman Asu da Kral Karadeniz a ranar 25 ga Janairu, 2010.)

“Kafirai mataimakan juna ne. In ba ku aikata ba fitina za  ta afku a bayan kasa da barna mai yawa.” (Suratul Anfal, aya ta 73)

“Mata wadanda ke da irin wannan tunani ba ka ganin su cikin masu kokarin tabbatar musulunci ta hanyar gwagwarmayar ilimi”

“Abinda nake fada game da dankwali (marufin  kai) na mata yana da matukar muhimmanci. Akwai ‘yan mata da yawa masu kishin addini. Ran nan wata matashiya ta zo waje na, kanta a kasa cikin kunya da kamun kai. Na ce da ita “Shin wace rawa ki ke taka wa a jihadin addini da kokarin yada addinin?” Ta ce “A’a.” Shin tana cikin wata kungiyar addini? Shi ma ta ce a’a. Na tambaye ta na ce me ya sa? Ta ce tsananin kunyarta shi  ya sa haka. To me ye burinta a rayuwa? Ta ce aure. “Ina son nima in sami iyali nawa.” Wannan hakika abin haushi ne. Shin yanzu lokaci ne da mace za ta zauna kawai a gida tana zaman aure? Shin haka matan sahabbai suka zauna kawai a cikin gidajensu? Matan sahabbai sun fito sun taka rawa a fagen jihadi. Aisha (ra) uwar muminai ta kasance tana tara matan sahabbai tana koyar da su ilim, kuma ta kan fita ta yi aikin isar da musulunci ga mushirikai da yahudawa. Shin ko ita ba kyakkyawar mata ba ce? Ta yi soyayya da Ma’aiki (saas) kuma ta yi aure don Allah da cika bautarSa. Amma kuma ba ta zauna kawai a gida ba, ta kasance cikin jihadi koda yaushe. To ko shi Ma’aikin Allah (Saas) bai yi zaman dirshan a gida ba, kullum yana cikin tafiye tafiye a kan tafarkin jihadi da yada addinin Allah. Shin ba haka ya kasance yana yi ba ne? Irin haka ya kamata musulmi su kasance. Amma sai ga shi suna zaune dirshan a gidajensu cikin kabilunsu.” (An ciro daga hirar Adnan Oktar da tashar Gaziantep Olay a ranar 30 ga Janairu, 2010.)

“Suna aibata masu aikin yada addini”

“Yayin da daya bangaren na musulmi ke kokarin addini da yada kiran Allah su kan gamu da aibatawa da cin mutunci a shafukan jaridu, inda a ke cewa suna yada ta’addanci. Shin kanka daya yake kuwa bawan Allah? Ka  yi aure kawai ka tara ‘ya’ya, shi ne burinka! Su kan ce in wa’azi ne ka yi wa ‘ya’yanka mana. Su kan ce suna da ‘ya mace ko biyu. Wannan a gurin su shi ne wa’azi ga mutane. An san Annabi (saas) ya yi wa’azi, to amma kai ba kamarsa ba ne. Shin ina ka samo wannan ra’ayi naka na yada addini? Batun “Umarni da kyakkyawa da kuma hani ga mummuna,” bai dace ba a wannan zamani. Wannan aikin Annabi (saas) ne ba naka ba. Su kan ce aikin mutum shine ya zauna a gida yana cin shinkafa da fisgar cinyar kaza yana korawa da shayi ko lemo. Wannan kuwa ya fi yin kama da kaucewa daga sahihiyar turba. Koda yake, akwai mutane da ke da kyakkyawar niyya a zukatansu, amma dolanci ya dakushe su. Wadannan ba sa cikin wadancan da na bayyana halayensu a baya. Kuskurensu a nan shine su kan yaudari kansu ta hanyar fakewa da wani abu da ke shagaltar da hankulansu wai da nufin samun nutsuwa. (An ciro daga hirar Adnan Oktar da tashar Kanal 35 da Kanal Avrupa ranar 31 ga Janairu, 2010.)


Musulmi a musulunci cike suke da shu’urin soyayya, da aminci inda suke zaune cikin fahimta da son juna. Duk al’ummar da ke da irin wadannan dabi’u ta fi saurin habaka da samun ci gaba. Har ila yau, wani babban abu shine wadanda ke kokari  tare da karfafa hadin kai da son juna Allah ya yi musu alkawarin taimako da  karfafawa. Shi ya sa a ayoyi da dama na Alkur’ani Allah ya ke gaya musu kada su rarraba, in suka yi haka sai karfinsu ya tafi kuma rauni ya mamaye su. Daya daga cikin ayoyin ita ce:
“Ku bi Allah da ManzonSa kuma kada ku yi jayayya a junanku sai ku tarwatse karfinku ya tafi. Ku yi hakuri. Allah yana tare da masu hakuri.” (Suratul Anfal, aya ta 46)

Kyawawan dabi’u da ya kamata a san musulmin kwarai da su

“Dabi’un Alkur’ani dole ne a gansu a aikace, ba kawai a karance ba”


“Maganar mayafi (lullubi) ta zo a cikin Alkur’ani a Suratun Nur da Suratul Ahzab, don haka ba abin da za mu kara a game da bayanin lullubi. Zan yi magana a kan wani abin daban. Don maganar lullubi ta fi shekara 1400 da samun umarninta. Irin mutanen da na ke ta magana a kan su suna sanya mayafi su rufe kansu, amma ba ruwansu da sallah, ko azumi ko kuma wani aikin addini. Sai dai an fi jin kan su wajen yada gulma da ayyukan batsa. Wadannan su nake suka, ka gane? Amma in banda wannan ba ni da wata matsala da sauran musulmi na kwarai. Akwai wani Hadisi inda Manzon Allah (saas) ya ke cewa “A karshen duniya za a sami mutane masu rawani dubu saba’in a tawagar Dujjal.” Ba wai ina kin rawani ba ne don kuwa Manzon Allah ya daura rawani a kansa.  Mun kasance ni da abokaina na tsawon shekaru muna sallah a masallatai da rawuna a kanmu, ko ban yi haka ba? Daga shekarar 1983 zuwa 87 mu kan daura rawuna mu sake su har gadon bayanmu don yin koyi da sunna, a haka mu ke sallolin jam’i a wancan lokacin, kowa ya sani. Ba ni da matsala a kan rawani in dai a masallaci ne, amma banda a cikin gari, tun da tsarinmu bai tafi a kan haka ba. Sa’annan tsaida gemu shi ma sunna ne, da ya zo daga Annabinmu (saas). Wasu mutane za ka gan su da dogayen gemuna, amma mutanen banza ne. Ba sa fatan tabbatar musulunci ko kokarin isar da sakon musuluncin. To me zan ce ga irin wadannan mutane? Kuma ta ya ya zan yi shiru bayan wadannan mutane suna ta tafka barna? Matan kuma za ka gan su da lullubi, amma ba abin da suka sa a gaba dare da rana sai gulma. Manufarsu a rayuwa su yi aure kawai. Su kan tsani ‘yan matan da ba sa lullubi, kamar su din wasu waliyyai ne. Amma watakila gara su ‘yan matan ma sau dubu da su ta fuskar tsarkin zuciya. Yarinyar da suke gani ba lullubi har suke tsanarta tana kasancewa ta shiga aljanna su kuma su fada wuta. Shi ya sa a addini ba a son alfahari da girman kai. Har sai mutum ya kasance mai kyakkyawar dabi’a da nuna soyayya, da tausayi da kuma yin rangwame ga mutane, kuma ya guji gulma da zunden jama’a.” (Daga hirar Adnan Oktar da tashar Gaziantep Olay ranar 30 ga Janairu, 2010.)

“Wadannan suna rigengeto zuwa ga alhairai, kuma za su tarar da su. Ba ma dora wa rai sai abin da za ta iya. A gurinmu akwai littafi wanda yake furuci da gaskiya. Su ba za a zalunce su ba.” (Suratul Mu’minun, aya ta 61 – 62).


“Wajibi ne ga mata musulmi su zama masu jarunta, mutunci da kokari a maimakon zaman dirshan da rashin katabus”

“Abu na biyu, shi ne matsayin mata musulmi tun da yake musulunci ya hada maza da mata ne, domin kusan matan ma sun fi yawa ko kuma rabi da rabi a ke. Tun ba yau ba a ke danne hakki da matsayin mata. A kan ce wai wacece ita? Ta ce ita ce mace. To me ye aikin ki? Aure. Sannan ki haifi ‘ya’ya, ki zama uwa, shi kenan! Ban da wannan ba ki da wani aikin kuma? Babu, shi ke nan. Sai dai ba haka ya dace ba, bai kamata mu rika takure rayuwar matanmu ba. Abu daya shine, wajibi ne ga mace musulma ta zama mai jarunta, mutunci da kokari. Wajibi ne ma mace ta fi namiji nuna juriya da kokari. Domin mata a bisa dabi’a sun fi kwarewa wajen iya sadarwa da isar da sakon musulunci. Don haka rawar da za su taka tana da matukar muhimmanci. Matar da ke maida kanta doluwa, ba ta amfanar al’umma da komai, me ye amfaninta! Dole ne matanmu su zamo masu lura da basira.” (Daga hirar Adnan Oktar da gidan talbijin na Adiyaman Asu da Kral Karadeniz ranar 25 ga Janairu, 2010).

“Wajibi ne mu guji rarraba a musulunci”

“Mafi yawan ‘yan matan musulmi ba sa shiri da junansu, inda har ta kai wasunsu ma ba sa yin magana da junansu saboda kawai bambancin kungiya da ra’ayi. Ita wannan tana cikin wannan kungiya, ita ma waccan tana da kungiyarta daban, don haka ba sa ma’amala da juna. Shin me ya sa haka? Saboda ra’ayinmu da nasu ba daya ba. Sai dai wannan ra’ayi namu da su din nan ba karamar illa yake kawo mana ba. Bari mu bada misali da daliban Suleiman Efendi; mazansu da matansu mutane ne masu gaskiya da kyawun dabi’a. Amma wani lokacin ba sa yin magana da junansu kawai saboda sabanin tunanni. Haka nan in muka dauki misalin daliban Nur, su ma wasu lokutan ba sa shiri da junansu. Su kan daukarwa kansu wani irin tsattsauran ra’ayi marar kan gado. Wannan kuwa sam ba daidai ba ne. Mu dauki misalin ‘yan mata daga cikin mabiya Fathullah Gulam – masu biyayya ta sau-da-kafa. Ko ba komai dai ‘yan uwanmu ne su. Amma kuma akwai wasu gungun mutane, wadanda saboda karatun jaridar Yeni Asya da su ke yi, suka daina magana ko gaisawa da junansu. Wannan wata baudaddiyar fahimta ce marar kyau. Alhalin an so ne da su rika son juna da taimakon ‘yan uwansu, a gansu har suna cin abinci tare. Kuskure ne mutum ya ce dole sai wani ya dauki irin ra’ayinsa. Kowa ya rike ra’ayinsa a girmama juna shine al’amarin gaskiya. Amma ka ce sai ka jawo wani ya watsar da ra’ayinsa ya dauki naka, sam ba daidai ba ne. Alal misali, bai da ce a tilasta wa kirista karbar musulunci. Hakkinka kawai shine ka yi masa wa’azi da cikakken bayanin samuwar Allah da dayantakarSa a tsanake. A na isar da sakon Alkur’ani ne cikin hikima ba da barazana ko karfi ba wadda za ta sa wanda a ke yi wa wa’azin ya kasa sakewa balle ya fahimci sakon. Kuma dole ka girmama na sa addinin, kuma ka saurari na sa bayanin. Babban laifi ne musulmi su shiga fada da gaba a junansu saboda sabanin ra’ayi kawai. Girmama juna shi ke jawo shakuwa har a sami fahimtar juna. Rashin tattaunawa shi ke jawo baraka da rashin hadin kan musulmi.” (Daga hirar Adnan Oktar da tashar Adiyaman Asu da Kral Karadeniz ranar 25 ga Janairu, 2010.)


“Ya ku wadanda suka yi imani idan kun  fita zuwa yaki a tafarkin Allah to ku bambance. Kada ku ce da wanda ya zo muku a musulmi ‘Kai ba mumini ba ne’ saboda kwadayin samun duniya. Allah a wajensa akwai ganima mai yawa. Kamar haka ku ka kasance a baya amma Allah ya yi muku tagomashi. Saboda haka ku bambance. Allah yana sane da abin da ku ke aikatawa.” (Suratun Nisa, aya ta 94)

“A maimakon neman ganin aibun juna, dole musulmi su rungumi hanyar hadin kai da son juna”

“Matsala ta uku ita ce yadda musulmi ke suka da cin naman ‘yan  uwansu. Matan kuwa su kan taru a gidajensu da sunan wani lamarin addini, amma sai su buge da gulma; wance ta yi kaza, su wane sun yi kaza... A maimakon bata lokaci a kan wadannan gumace gulmacce, me zai hana su yi tunanin kalubalantar zindikancin masu ra’ayin Darwin da ýan akidar zahiranci (materialists)? Ko su rika ilmantar da juna kan sha’anin addini da ya shafi imani, tsoro da kuma son Allah. Amma don me wasu musulmi za su taru suna cin naman ‘yan uwansu musulmi? Misali, akwai wani majalisi da a ka yi a wani wuri, inda bayan an karanta littafin Risalat Nur sai kuma a ka shiga gulma da zunde. Ba na ce kowa ne ke yin hakan ba, amma dai da dama haka a ke yi. Ba wanda ke son a rika yi da shi bayan idonsa. To in haka ne meye amfanin gulma, in banda hali ne na mutanen banza. Bai kamata mutane su rika cin naman junansu ba; zai fi kyau su so juna tare da girmama juna, ta haka ne Allah zai taimake su. Su kasance masu fadin “Ya Allah, ka haskaka duniya da haskenka, ka gaggauto da tabbatar musulunci a duniya, ya Allah a cikin wannan karni.” Irin addu’o’in da ya kamata su rika yi kenan don neman taimakon Allah da daukinsa. Shin a baya ka taba ji ana maganar soke bizar shiga kasashe ko batun hadin kan duniyar musulmi? Amma yanzu akwai muhimman ci gaba da a ka samu musamman wajen yunkurin kafa cibiyar hadin kan musulmi ta Turkiya. Lokacin da na fara magana kan wannan al’amari kimanin shekaru biyu da suka gabata, mutane sun yi ta mamakin abin da na ke fada, saboda ba su taba zaton haka ba. In da za ka duba jaridun wancan lokaci, za ka ga ba wani abu da suka buga game da wannan al ;amari don kuwa da niyya suka ki bugawa. Amma abubuwa sun canja yanzu.” (An dauko daga hirar Adnan Oktar a tashar Gaziantep Olay ranar 30 ga Janairu, 2010.)

Musulmi ba sa gudun wahala a tafarkin Allah. Dole musulmi su sallama kansu gaba daya”

“Su kan ce kullum wuridin safe da na yamma ba sa wuce su. Mata kuma kan ce kullum ba sa rabuwa da dankwali. Kuma sallah, su kan ce a koda yaushe a kan lokaci suke yinta. Kwarai wannan abu ne mai kyau, sai dai  kowa ma yana yin haka. Mace tana iya daure kanta da dankwali a tsakar gidanta, ta kuma bada faralinta a dakinta. Matashi kan shiga makaranta, har ya kammala karatunsa, sannan ya yi aure,  ya maida  hankalinsa kan aiki da iyalinsa. To amma irin wannan ba ita ce siffar musulmin da Alkur’ani ya bayyana ba. Shi musulmi yana sallama kansa ne gaba daya ga Allah mahaliccinsa, kuma yana yin hakan ne ta hanyar nisantar jin dadin rayuwa mai rudi. Domin Manzon Allah (saas) ya gujewa dadin duniya ya sadaukar da rayuwarsa a hanyar bautar Allah. Shin ba ka jin da Annabi (saas) ya ga dama shi ma da sai ya yi zamansa a gida, amma ya fito zuwa hijira don bin umarnin Allah, har ya zauna cikin kogo? Ya yi tafiye tafiye masu yawa inda har Habasha sahabbansa sun je a tafarkin hijira saboda daukakar addinin Allah. Hanyoyin sun kasance masu hatsarin gaske, amma haka suka yi dogon zagaye ta sassan Afirka. Yara ‘yan shekaru 15 zuwa 16 duk sun amsa kiran Manzo suka yi hijira inda suka tafi suka bar iyalinsu don daukakar addinin Allah. Ga sauran matasa kuwa sai su ce “kun kyauta, kun cika masu wayo. Kun cika masu biyayya da soyayya ga iyalenku tunda ba ku bi Muhammad (saas) ba. Wannan shine matukar sanin hakkin iyali. Ga ki yarinya mai saukin kai, mai kawaici da tsaida sallah, ga ki mai ilimi, kuma ga aikinki kina yi, to me ye naki na shiga wata  harkar jihadi! Haka kuwa wasu suka zauna ba su bi Manzon Allah (saas) ba; gani suke sun fi kowa wayo. Su kuma sahabbai suka bi manzo suka yi hijira, kuma suka sami rabo a wannan duniya da kuma na lahira mai zuwa. Mu kuwa yanzu ai ko sawunsu ba ma ganowa, ko ba haka ba? Ladan su a lahira dauwamamme ne.” (An ciro daga hirar Adnan Oktar a tashar Talbijin ta Samsun Aks da Kayseri ranar 27 ga Janairu, 2010.)

Wajibi ne musulmi su tsare hakki da taimakon junansu. Dole ne su guji dabi’ar nan ta kiyayya da juna saboda dalilin kungiya, kabilanci ko bangaranci. Koda yake wannan ba zai hana in an ga wani bangare yana kan kuskure ko bata a dauki matakan gyarawa ba. Misali, nuna adawa da kokarin tabbatar tsarin musulunci babban laifi ne da ke bukatar daukar mataki a kai. Ko kuma in a ka ga wani yana  fassara ayoyin Alkur’ani bisa son rai, to abu ne da mmusulmi ba za su yi shiru suna kallo ba. Amma banda haka, zai yi kyau musulmi su riki harshe guda da zai karfafa soyayya da hadin kansu.” (An ciro daga hirar Adnan Oktar a tashar Adiyaman Asu da Kral Karadeniz ranar 25 ga Janairu, 2010.)


“Musulmi wajibine ya zama neman yardar Allah shine babban burinsa”

“Manufa da burin mutum  ya kasance neman yardar Allah da rahamarsa a birbishin kowace manufa. Musulmi kan je makaranta ko wurin aiki, ya nemi aure, har ya yi gudun hasara. Kamar dai in ce ne, duk daya gare ni, da na so sai in zauna gida abina. Ka ga kenan ba mai kama ni, balle a daure ni har labari ya bazu a jaridu cewa an kama ni. Haka nan ba mai kaini asibitin mahaukata, ko a tsaida ni gaban kotu in fuskanci hukunci. Ba wani abin ki da zai same ni. Ka ga sai in maida hankalina sosai a kan harkokin kasuwanci na. Amma kuma a karshe  ina iya shiga wuta a ranar lahira, Allah ya kiyaye. Saboda haka ba karamin wauta ba ce mutum ya zaci yin hakan wani wayo ne; wato mutum ya rika yi wa wadanda suka sadaukar da rayukansu a jihadin neman yardar Allah a matsayin wawaye, sannan ya rika daukar kansa shine wayayye, bayan kuma a hakika ba haka ba ne. Rayuwar wannan duniya takaitacciya ce. Ba mun zo duniya ba ne kawai don a haife mu mu haifa, mu ci mu sha kamar dabbobi ba. Shi mutum in an haife shi a na nufin ya taso da bautar Allah, ya kasance bawan Allah mai neman yardar ubangiji ta hanyar aiki da koyarwar Alkur’ani, sannan ya ke fatan dacewa da shiga aljanna a ranar gobe kiyama. Badiuzzaman Said Nursi (shahararren malamin musulunci) bai shafe shekaru talatin a gidan kurkuku wai don ba shi da wayo ko dabara ba ne. A daidai lokacin da yake garkame a kurkuku na tsawon wadannan shekaru talatin yana shan bakar azaba, musulmi da ke waje sun ci gaba da yin azumi, da harkokin kasuwancinsu, suna ci suna sha tare da jin dadi da matansu! Amma kuma wai suna ganin kamar matsayinsu daya da shi da ya sha wahala a tafarkin Allah. Sam ba haka ba ne. Allah zai tambayi kowanensu a ranar lahira. Ma’ana Badiuzzaman shine a kan tafarki madaidaici saboda kokarinsa na daukaka addinin Allah sabanin ‘yan zaman dirshan. Don haka, mutum mafi wayo da hikima shine wanda gaba daya ya mika wuyansa ga Allah mahalicci.” (An dauko daga hirar Adnan Oktar a tashar Samsun Aks da Kayseri ranar 27 ga Janairu, 2010.)
 

2010-04-21 10:50:15

Bayani akan shafin | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to author “Mr. Adnan Oktar”.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top
iddialaracevap.blogspot.com ahirzamanfelaketleri.blogspot.com ingilizderindevleti.net