YADDA MOMINAI SUKE KALLON RAYUWAR DUNIYA

“Rayuwar duniya ba komai ba ce sai wasa da wargi. Lahira – wannan ita ce rayuwa ta hakika, in da sun san haka. (Suratul – Ankabut, aya ta 64)

Allah ya halicci wannan duniya a matsayin mazauni na wucin-gadi don ya jarrabi mutum, ya tsarkake shi daga munanan ayyukansa, ya sanya shi mai tsarkakakke kuma madaukakin ruhi wanda zai kai shi ga samun aljanna, sannan kuma don ya bayyana siffofin kafirai da ayyukansu. Sai dai ‘yan kalilan  ne daga cikin mutane suke yin tunani da lura har su fahimci manufar Allah a cikin lamarin duniya; wadannan kuwa su ne masu imani.

Saboda haka, mutum mumini wanda ya yi imani yana kallon duniya ne ta wannan mahanga wadda Alkur’ani ya bayyana. Bambancinsu da kafirai wadanda ba su da darsashin imani tare da su shine, shi mumini ba ya damfara kansa da rayuwar wannan duniya, sai dai yana kokarin nemarwa kansa kyakkyawar makoma a gobe kiyama. Da ya ke ya san an halicce shi ne “don ya bautawa Allah shi kadai,” don haka a koda yaushe ya ke tuna ayar nan da ke fadin “Ban halicci mutum da Aljan bs sai don su bauta min.”(Sura Zariyat, aya ta 56)Bautar Allah kuwa ba ta takaita ga aikata wasu nau’o’in bauta ba ne kawai kamar kiyaye salloli da yin azumi. Amma abin da ake nufi shine gaba dayan rayuwar bawa ta zama a cikin bautar ubangijinsa ya ke tafiyar da ita. Saboda haka, cikakken mumini shine mutumin da ya tafiyar da gaba dayan rayuwarsa a cikin bautar Allah. Ya san cewa wannan duniya gidan jarrabawa ce, kamar yadda a cikin Alkur’ani Allah ya jawo hankalin mutane ga wannan al’amari cewa: “Hakika mun halicci mutum daga gaurayayyen diyon maniyyi don mu jarrabe shi, sannan muka sanya shi mai ji da gani.” (Suratul Insan, aya ta 2)

Bugu da kari kuma, Allah yana jawo hankalinmu dongane da rudin rayuwar duniya in da ya ke gargadinmu da cewa:

“Ya ku mutane! Alkawarin Allah gaskiya ne. Kada rayuwar duniya ta rude ku kuma kar mai rudi ya rude ku a cikin al’amarin (bin) Allah.” (Sura Fatir, aya ta 5)

Muminai su ne wadanda kyawu da alatun rayuwar duniya ba sa rudar su, duk kuwa da tsananin kyawu da daukar rai da suke da shi. Dalilin wannan kuwa shi ne saboda littafin Allah ya yi musu bayanin sirrin rayuwar wannan duniya filla filla. Kamar yadda Alkur’ani ya ke bayyana mana, ita rayuwar duniya “wasa ce” da “shakatawa” “da ado” “da alfahari a tsakanin mutane” “da kuma gasar tara dikiya da ‘ya’ya.” A cikin wannan aya ta Alkkur’ani, Allah ya buga mana misali wanda ya fayyacce mana matsayin wannan rayuwa ta duniya:

“Ku sani cewa rayuwar duniya wasa ce, da shantakewa, da ado, da alfahari a tsakaninku da kuma gasar tara dukiya da ‘ya’ya. Kamar misalin ruwan sama ne (wanda a sakamakonsa) yabanya ta fita kyawunta ya burge manoma, sannan sai  ta bushe ka ganta ta koma ruwan dorawa sannan ta zama karmami (a warwatse). A ranar lahira akwai azaba mai tsanani da kuma gafara daga Allah da kuma yardarSa. Rayuwar wannan duniya ba komai ba ce face jin dadi na rudi.” (Suratul Hadid, aya ta 20)

Kamar yadda wannan misali ya nuna mana, babu wani abu a wannan duniya face sai ya gamu da tasirin shudewar zamani; komai inganci da kyawun gidaje, da tsala tsalan motoci masu daukar ido, ko lambunan debe kewa masu kyawu, ko kuma matasa masu zalaka a wurin aiki ko sana’o’insu, babu mai iya kubuta daga tasirin shudewar zamani. Komai sabuntar abu zai koma tsoho, matasa majiya karfi da shu’urin rayuwa su zama tsofaffi. Zamani ke hallaka abubuwa masu daraja a idon dan-adam ya maida su marasa daraja da muni. Lokacin da mutum ke ganiya da holewarsa nan da nan kuma sai ya shude ya zama tarihi kamar ba a yi shi ba. Bayan wani lokaci kuma duk wani abu mai daraja ko jin dadi sukan kasance an manta da su. A wata aya Allah yana sanar da mu irin shu’urin da ke sa wa mutum son rayuwar duniya:

“An kawata wa mutum tsananin sha’awa ga mata da ‘ya’ya, da tarin (dukiya ta) zinare da azurfa, da dawakai na kawa, da dabbobi da gonaki. Wadannan jin dadi ne na rayuwar duniya. Amma ga Allah kyawun makoma yake.” (Sura Al’Imrana, aya ta 14)

Muhimmin abin da za mu fahimta a cikin wannan aya da ta gabata shine, cewa ni’imomin duniya yankakku ne ba masu dorewa ba. Don haka bai kamata ga mutum ya kallafa rayuwarsa a kan wani abin cikin wannan duniya ba, domin kuwa ma a bisa al’ada da halittar mutum ta zahiri wadda ta kunshi kashi da tsoka, har sauran abubuwan duniya marasa daraja da dorewa, babu abin da zai sa su baiwa mutum damar kallafa rayuwarsa ga wannan duniya baki daya. Irin ni’imomin da mu ke gani a wannan duniya wani dan yanki ne daga ni’imomin aljanna da a ka gutsuro mana don tuna mana ranar lahira.Masu imani wadanda suka fahimci wannan manufa su kan ci ribar rayuwar wannan duniya. Amma akwai wani abu guda da ya bambanta su da sauran wadanda suka rudu da rudin duniya; saboda su muminai ba sa nuna hadama a kan ni’imomin duniya. A maimakon haka ma, a koda yaushe cikin godiyar Allah suke saboda baiwa da ni’imomin da ya yi musu, domin sun san cewa hakikanin mamallakin komai na duniya shine Allah.

Wadanda ke ganin wai sun mallaki dukiya, ko suna da halitta mai kyau, ko kuma suna da karfin mulki a hannunsu, to hakikanin gaskiya suna yaudarar kansu ne, tun da ba su ne suka halicci wadannan abubuwa da suke tinkaho da su ba. Hasali ma, ba su da ikon halittar koda abu guda daya daga cikinsu, haka  kuma ba su da ikon kare abubuwan daga lalacewa ko halaka. Su kan su ababen halitta ne da a ka halicce su.... kuma wata rana mutuwa za ta riske su, su tafi su bar duk abubuwan duniya da suka mallaka. In muka lura da wannan aya da ke cewa “Wadannan mutane suna kaunar rayuwar wannan duniya kuma suka sanya tunanin rana mai nauyi (lahira) a bayansu,” (Suratul Insan, aya ta 27) za mu gane abin da ya bambanta muminai masu yakini da kuma wadanda suka shantake a rayuwa, domin muminai a koda yaushe a cikin shirin fuskantar rayuwar gobe kiyama suke ba ta wannan duniya ba. Alkur’ani ya kawo mana irin addu’o’in da su ke yi:

“Daga cikinsu kuma akwai masu cewa ‘Ya Ubangijinmu, ka ba mu kyakkyawa a duniya da kuma kyakkyawa a lahira, kuma ka tsare mu daga azabar wuta.” (Suratul Bakara, aya ta 201)

A sakamakon iklasinsu da addu’o’in da suke yi, sai Allah ya hada musu ni’imar duniya da ta lahira baki daya. A cikin Alkur’ani Allah ya yi albishir a kan haka:

“Saboda haka Allah ya ba su sakamako na duniya da kuma mafi kyawon sakamakon lahira. Allah yana son masu kyautatawa.” (Sura Al’Imrana, aya ta 148)

“Akwai bushara gare su a rayuwar duniya da kuma a lahira. Babu sauyi a maganar Allah. Wannan shine rabo mai girma.” (Sura Yunus, aya ta 64)


2010-04-07 07:38:53

Bayani akan shafin | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to author “Mr. Adnan Oktar”.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top
iddialaracevap.blogspot.com ahirzamanfelaketleri.blogspot.com ingilizderindevleti.net