RAYUWAR MUTUM JARRABAWA CE


Allah ya halicci kowane abu a bisa hakikanin ikonsa, kuma ya hore wa mutum sarrafa sauran abubuwan da ya halitta a duniya. A bayyane yake cewa halittar Allah da yawa a sararin wannan dunya, tun daga kan halittu irin su rana da wata, zuwa ga nau’o’i na iskoki da ke cikin sararin subhana, haka nan daga dabbobin ni’ima wadanda muke samun nama da madara daga jikinsu zuwa kan ruwa, duk an halicce su ne saboda jin dadi da kuma amfanin mutum. Idan har a ka fahimci hakikanin wannan bayani a matsayin hujja, to zai kasance kenan rashin tunani ne mutum ya dauka wannan rayuwa haka take kara zube ba ta da manufa. Tabbas kuwa akwai manufa a cikin wannan rayuwa, kamar yadda Allah ya fada:

Ban halicci mutum da Aljani ba sai don su bauta min. (Suratuz – Zariyat, aya ta 56)

‘Yan kalilan ne kawai daga cikin mutane suke fahimtar wannan manufa ta rayuwa har kuma su tafiyar da rayuwarsu a kan wannan manufa. Allah ya halicce mu a bayan kasa ne don ya jarrabe mu a kan shin za mu bi tsarin dokkin da ya tsara mana ko kuma za mu fandare. Tun a nan duniya a ke banbancewa tsakanin bayin Allah masu bauta ta hakika da kuma wadanda suka yi tawaye ga dokokinsa. Duk ni’imomin da Allah ya yi wa mutum (na halittar jikinsa, da sanya masa tunani da kuma sauran ni’imomi marasa iyaka) abubuwa ne da Allah ya ke jarraba mutum da su. A wata ayar Alkur’ani, Allah yana cewa:

Hakika mun halicci mutum daga digon maniyyi gaurayayye don mu jarraba shi. Kuma muka sanya shi mai ji da gani. (Suratul – Insan, aya ta 2)

Aiki ko nauyin da a ka dora wa mutum a rayuwar wannan duniya shine cewa ya yi imani da Allah da ranar lahira, ya tafiyar da rayuwarsa a bisa koyarwar Alkur’ani, ya kiyaye iyakokin Allah, da kuma neman yardarsa. Jarrabawar da ke samun mutum a tsawon rayuwa ita ke bayyana wadanda suke tsaye a kan tafarki. Tun da yake kyakkyawan imani da iklasi – imani irin wanda ke ratsa jiki da zuciya amma ba irin wanda mutum zai furta da baki cewa “Na yi imani” kawai ba – shi Allah yake bukata daga bayinsa, don haka ya wajaba ga mutum ya tabbatar yana da imani sahihi, ta yadda babu ta inda yaudarar shaidan za ta ci galaba a kansa har ya kauce daga tafarkin addini. Har ila yau, wajibinsa ne ya tabatar ba ya bin hanyar kafirai batattu, ko kuma daukaka bin son  ransa a bisa neman yardar Ubangiji. Ayyuka da yanayin halayyar mutum a duniya sune za su tabbatar da haka. Allah yana jarraba mutum da halin kunci ko wata masifa, inda ta hanyar juriya da hakurinsa ne a ke gane matsayin imani da sadaukarwar mutum a sha’anin addini. Allah ya yi bayanin wannan a cikin Alkur’ani mai girma kamar haka:

Shin mutane suna zaton za a kyale su haka nan don sun ce “Mun yi imani” ba tare da an jarrabe su ba? (Suratul – Ankabut, aya ta 2)

A wata ayar kuma Allah ya gaya mana cewa wadanda suka ce “Mun yi imani” sai an jarraba su:

Shin ko kuna zaton za ku shiga Aljanna ba tare da Allah ya san wadanda suka yi kokari daga cikinku da kuma wadanda suka yi hakuri (juriya) ba? (Al’Imrana, aya ta 142)

Saboda haka, a bisa hakikanin lamari, yin bakin ciki ko debe kauna yayin tsanani ko jarraba abu ne da bai dace mutum ya yi shi ba. Wannan kunci kuwa ya kan kasance ta hanyar manyan bala’ai ko kuma matsalolin yau da kullum na rayuwa. Saboda haka wajibi ne ga wanda ya yi imani da ya dauki wadannan al’amura da kan same shi a matsayin wani bangare na jarrabawar da a ke yi masa, kuma ya dogara ga Allah da kuma neman yardarsa a koda yaushe. A wannan aya ta Alkur’ani, Allah yana bayyana mana irin kuncin da a ke jarrabar muminai da su kamar haka:

Tabbas za mu jarrabe ku da wani yanki na tsoro, da yunwa, da kuma hasarar dukiya, da rai da ta amfanin gona. Kuma ka yi bushara ga masu yin hakuri. (Sura Bakara, aya ta 155)

Haka kuma Manzo Muhammad (S.A.W.) ya tunatar da muminai da cewa, “Duk wanda ya yi hakuri da ita (jarrabawar da ta same shi) zai sami yardar Allah. Wanda kuma ya kasa yin hakuri da tawakkali zai gamu da fushin Allah.” (Tirmizi)

Ba da halin kunci ko wahala ne kadai a ke jarrabar mutum a wannan duniya ba, hatta halin ni’ima ko wadata su ma a kan jarrabi imanin mutum da su. Allah ya na jarraba mutum da kowace irin falala  ko ni’ima da ya yi masa don ya ga shin zai nuna godiya ko zai butulce ne. Kamar yadda Allah yake bijirowa da al’amura wadanda ke haifar da tasiri a tunani da ra’ayin mutum, saboda haka a halin jarrabawar da mutum ya sami kansa ya kan zama ko dai mai biyayya da dokokin Allah da neman yardarsa, ko kuma mai bin ra’ayin da ransa ya saka masa. Yayin da mutum har ya iya fahimtar halin da yake ciki cewa jarrabawa ce daga Allah, to wannan za a iya cewa ya yi nasara. Amma kuma in har lamuransa a wannan hali ya biyar da su ne a bisa sha’awa da rudin ransa, to ya jefa kansa cikin aikata zunubi wanda zai yi nadamarsa a ranar lahira, kuma zai kasance cikin yamutsi da rashin kwanciyar hankali a rayuwar duniya.

Tabbas, kamar yadda muka bayyana, Allah ya halicci komai a wannan duniya ne a matsayin jarrabawa ga mutum. Irin abubuwa da al’amuran da jahilai suke gani kamar suna faruwa ne a bisa katari ko tsautsayi, to a hakika al’amura ne da suke faruwa a bisa nufi da kaddarawar Allah ta’ala. Daga cikin wannan, Allah ya bada misali da Yahudawa da suka karya dokar hana su yin su (kamun kifi) ranar asabar, sakamakon bin son zuciya:

Ka tambaye su game da Alkarya (gari) wadda ke gefen kogi, yayin da suka karya dokar Asabar – yayin da kifayen ke zuwa musu a ranar da a ka hana su kamun kifi (asabar) amma ranar da babu dokar ba sa zuwa musu. Ta haka muka jarrabe  su saboda sun kasance masu kaucewa daga hanya. (Sura A’raf, aya ta 163)

Watakila yahudawan sun yi zaton zuwa musu da  kifayen suke yi a ranar asabar bisa “katari” ne, sai dai kuma lamarin ya kasance tsararre ne daga Allah a matsayin jarraba gare su. Kamar yadda wannan hikaya ta nuna karara, a cikin kowane yanayi ko al’amarin rayuwa da ke faruwa akwai manufar Allah da kuma jarrabawa. Duk abin da ya sami mumini abu ne da Allah ya hukunta zai same shi don ya fahimci hikima da manufar Allah a cikin lamarin, ya fuskanci jarrabawar da juriya da tawakkali, sannan ya dora dabi’a da rayuwarsa gaba daya a bisa dokokin da Allah Ubangiji ya shimfida masa.
2010-03-27 08:58:19

Bayani akan shafin | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to author “Mr. Adnan Oktar”.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top
iddialaracevap.blogspot.com ahirzamanfelaketleri.blogspot.com ingilizderindevleti.net