A KODA YAUSHE A KAN GA FARIN CIKI A FUSKOKIN MUMINAI WANDA KE BIJIROWA SABODA SANIN CEWA KOWANE ABU AN HALICCE SHI NE AKAN MANUFA

Allah ya halicci kunci ko jarrabawa a rayuwar duniya ta yadda sai bayinSa da ke aiki da hankula da kwakwalensu ke samun rayuwar farin ciki. A cikin hikimar wannan jarraba akwai kyakkyawa kuma sassaukan tsarin manufa mai saukin fahimta da sabuntawa. Amma wadanda ba sa yin duba da idon basira, irin wanda Allah ya bayyana mana a cikin Alkur’ani, wadanda kuma ba sa lura da abubuwan da suka zo a cikin Alkur’anin, ba za su iya fahimtar wannan sassaukar manufa da ke boye cikin jarrabawar ba. Saboda haka suke shafe yawancin rayuwarsu cikin yanayin kunci da tashin hankali; wato rayuwa marar amfani mai cike da yawan damuwa da bakin ciki. Duk lokacin da wadannan mutane suka sami kansu cikin mawuyacin hali, su kan dube shi a matsayin bala’i da ba shi da magani ko mafita. Tabbas irin wannan tunani yana nuna fita daga hayyaci da toshewar basira, wanda tasirinsa kan sanya masu wannan siffa su debe kauna ta yadda ba sa zaton samun kansu cikin wani yanayi daban sabanin wannan mawuyacin da suke ciki.

Amma hakikanin lamari shine, duk wanda fahimtarsa ga jarrabawa da kunci na wannan rayuwa ta duniya tana bijirowa ne daga mahangar Kur’ani, to ba za ka taba ganinsa cikin rudu da daburcewar al’amura ba, ko ka gan shi kullum cikin kunci da tashin hankali irin na rashin nutsuwar zuciya ba. Akwai wasu al’amuran hakika wadanda duk mutumin da ya yi imani da Allah zai gaskata su kai tsaye. Wannan ilimi kan taimaka wa mai imani wajen yanke hukunci da ya dace da kyakkyawar koyarwar Alkur’ani ta hanyar yin amfani da tunaninsa. Bayanan hakika na Kur’ani su kan yi tasiri ga wanda ya gaskata su a dukkan al’amuransa na yau da kullum. Idan mutum ya ci karo da matsaloli ko wahalhalun rayuwa, to tunda kuwa ya gina rayuwarsa ne akan koyarwar Alkur’ani mai tsarki, babu wata jarrabawa, wahala ko kunci a fadin wannan duniya da zai hadu da su, duk kuwa tsanani da girmansu, face sai sun zo masa da sauki kuma ya sami maganinsu. Irin al’amuran rayuwar da ke haddasa mummunan bakin ciki, da bacin rai ko tashin hankali da kuma da-na-sani ga mutanen da babu darsashin imani a zukatansu, a hakikanin gaskiya su kan sanya nutsuwa da farin ciki ga ma’abota imani, da yake sun yi riko da kyakkyawar mahanga.

Kamar yadda a ka bayyana a sama, dalilin samun wannan sabanin fahimta ta mahanga a tsakanin muminai da  marasa imani shine saboda su muminai sun kasance masu ilimi da kuma bada gaskiya da abin da ke cikin Alkur’ani mai girma. Hakan kuwa ya kasance ne saboda sani da kuma imaninsu akan cewa:

• Allah iliminSa ya game komai,

• Allah mai matukar adalci ne,

• Allah shi ya halicci duk wani abu da ke bayan kasa, babba ko karami,

• Allah mai matukar jinkai ne, mai son bayinSa da yin gafara gare su

• Allah yana amsa dukkan rokon bayi a gare Shi da mafi kyawun sakamako,

• Allah yana fitar da bayinSa daga halin kunci da masifa,

• Mika al’amuranmu ga Allah Ubangijinmu, masani mai tsananin hikima da adalci, da rahama da soyayya ga bayinSa, it ace hanyar lumana,

• Mutane suna rayuwa ne kan abin da aka kaddara musu, kuma koda za su rayu a duniya marra dubu, ba za su wuce kadarinsu ba wanda Allah masanin halitta ya tsara musu,

• Duk abubuwan halitta da mutane suke gain a sararin duniya ba zaman kansu suke yi ba; komai nasu yana gudana ne da umarni da kuma ikon Allah da ya kage su,

• Allah shi ke azurta muminai ya kuma hore musu hikima da mafita a dukkanin al’amura,

• Kyakkyawan al’amari ko mummuna yana zuwa ne daga nufin Allah, mutane ba su da iko akan tunkude sharri ko jawo alheri akansu,

• Bai halatta ga mutane su rika gaba da junansu ba, domin cewa su kaskantattu ne kuma raunanan halitta wadanda ke rayuwa a bisa iko da kaddarawar Ubangiji, kuma ba su da ikon yin komai sai abin da ya nufe su da shi,

• Mika wuya ga Allah da bada gaskiya da hukuncinSa, da yin nazarin falala da kuma hikima a cikin al’amarin halittu, wajibi ne kamar yadda Alkur’ani ya bayyana,

• Haka nan kuma, babu batun bakin ciki, da kunci ko debe kauna a tafarki na koyarwar Alkur’ani,

• Tashin hankali da wahalhalu su kan kasance wata rahama ce ta fuskar samun lada a ranar lahira, kuma nuna juriya a halin wadannan wahalhalu alama ce ta karfin imani,

• Ya zo a cikin Alkur’ani cewa za a jarrabi masu imani da tsananin al’amura a rayuwa, saboda haka wahalhalun da mutum ya sami kansa ciki gaskatawar abin da ayoyin Kur’ani suka nuna ne,

• Gurace guracen duniya makiya ne da ke halakar da mutum. Don haka yakar son zuciya saboda imani da fifita son Allah akan komai yana samar da babban matsayi a gurin Allah,

• Shaidan ya yi alkawarin batar da mutum, don haka yake yin amfani  da alatun duniya don ya shagaltar da masu imani. Sai dai kuma Allah ya tsare musulmi daga fadawa tarkon rudinsa,

• Bala’i da wahalhalu da ke samun muminai a rayuwar wannan duniya su kan kasance wata dama ce gare su don jaddada soyayyarsu da kuma mika wuya ga Ubangiji,

• Yardar Allah ta fi kowace iri baiwa ko ni’ima da mutum zai samu a wannan duniya,  yayin da kuma Allah zai tabbatarwa da masu imani rayuwar farin ciki da nutsuwa wadda ta zarce duk wata ni’imar duniya da za su samu.

Koda mutum ya kasance mafi farin jini a duniya kuma koda ya mallaki komai na rayuwa irin wanda ransa yake so, duk da haka zai iya kasancewa  ya rasa kwanciyar hankali da jin dadi idan – Allah ya kiyaye – Allah yana fushi da shi. Amma kuwa in ya rungumi rayuwa da dabi’a masu kyau wadanda ya san Allah ya yarda da su, sannan ya dage a kan imani da mika wuya ga Allah da kuma sallama al’amuransa gareshi a cikin kowane irin yanayin rayuwa da ya sami kansa a ciki na kunci ko wahala, to wannan zai more rayuwar farin ciki da aminci da bai taba samun irinta ba a rayuwarsa, koda kuwa sauran mutane suna kin sa. Kuma a kan gane mutumin da ke cikin irin wannan rayuwa ta zahirinsa da kuma yanayin tunaninsa. Muhimmai daga cikin wadannan alamomin da a kan gane shi sun hada da:

• A kan ga alamun farin ciki da hasken imani a fuskarsa.

• A kan ga yanayin farin ciki, tunani da kuma babi’arsa ba sa canjawa a cikin halin ni’ima ko kunci.

• Ba a ganin alamun kasawa a magana da dabi’unsa. Ba ya furta kalaman da suka sabawa koyarwar Alkur’ani, ko nuna halayyar rashin imani da yin tawaye ga Allah mahalicci. Haka kuma ba a jin lafazan debe kauna da gushewar tunani wadanda suka sabawa Kur’ani, a cikin kalamansa.

• A kullum halayyarsa ta da’a ce ga Allah Ubangiji, kuma kyawawan dabi’unsa koda yaushe su kan nuna tsantsar imani da mika wuyansa ga Allah, kamar yadda ya  ke da imani a kan cewa akwai amfani da manufa a cikin halittar kowane abu, da kuma cewa mutane da gabadayan al’amura suna karkashin iko da kulawar Allah mahalicci mai taimakon muminai.

• Ya yi imani da cewa rayuwar wannan duniya takaitacciya ce (kamar cin kasuwa), inda kuma rayuwar lahira ita ce matabbata ga masu imani. Saboda haka ba ya damuwa ko ya yi bakin ciki saboda rashi ko hasarar wata ni’ima ko kayan alatun duniya. Sannan ya yi imanin cewa abin da ya rasa na ni’imar rayuwar duniya zai zame masa alheri ne a lahira. Sakamakon haka duk wani kunci ko masifa da ta same shi a nan, ni’ima ce gare shi a can.

• Duk irin tsananin hasara ko kunci da ya shiga, zuciyarsa tana cike da dangana da kyakkyawan fata na samun soyayyar Allah da kuma yardarsa, wanda samun wannan ya fi masa samun duk wata ni’imar duniya.

• Mutumin da ya san kowane abu da manufa a ka yi shi, kuma ya san cewa jarraba da kunci suna zuwa ne daga Allah, sannan ya fuskance su da imani da tawakkali zai kasance mai nuna soyayya ga sauran halittu. Tun da yake ba a raba mumini da adalci, tare da farin ciki da son daidaito, don haka ya kan kauda kai da yin afuwa ga wadanda suka cuce shi ko suka ci zarafinsa ta hanyar nuna kauna a gare su. Babu abin da ke kautar da shi daga kan koyarwar Alkur’ani, don haka fushi da kiyayyar mutane ba sa yin rinjaye a kansa. Ya san cewa kura kuran da mutane  ke aikatawa haka Allah Ubangiji ya kaddaro musu don a nuna musu su gane gaskiya. Shi ya sa ba a ganin mummunan nufi a cikin mu’amalarsa da sauran mutane. A sabanin haka ma, saboda zurfin imanisa a koda yaushe ya kan nuna soyayya da tausayawa a dukkanin mu’amalolinsa da sauran mutane.

2010-03-05 19:49:03

Bayani akan shafin | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to author “Mr. Adnan Oktar”.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top
iddialaracevap.blogspot.com ahirzamanfelaketleri.blogspot.com ingilizderindevleti.net