Musulunci Ya La'anci Ta'addanci

DOWNLOAD THE BOOK

Download (DOC)
Comments

CHAPTERS OF THE BOOK

< <
8 / total: 10

Illar ilimin Bangare daya na Darwiniyanci

Ta hanyar yada karyar cewa babu manufa a rayuwar mutum, mabiya Darwiniyanci sun maida mutane zuwa mutane masu cutar kwakwalwa, masu mummunan zato da hauka, wadanda kullum ba su kyakkyawan fata ko farin ciki.

Daya daga cikin misalan wannan shine Anders Behring Breivik, dan kasar Norway. Breivik ya yi ikrarin aiwatar da ayyukan ta'addanci guda biyu a kasar Norway aranar 22 ga Yuli, 2011. Daya daga ciki shine harin bam a kan ginin gwamnati a birnin Oslo inda mutane 8 suka rasa rayukansu. Dayan kuma hari ne akan sansanin matasa na jam'iyyar Ma'aikata a tsibirin Utoya. Mutane sittin da tara suka mutu a cikin harin.

Kafin hare haren, Breivik ya fitar da ra'ayinsa a cikin littafinsa mai suna "European Independence Manifesto." A shafi na 1518, ya bayyana cewa ya dauki kansa a matsayin gwarzo, mai nasara na ra'ayin kimiyyar duniya da kuma ilimin halittar rayuwa na zamani. Daga cikin littattafan da ya fi "dauka da daraja" shine origin of Species (Asalin Nau'in Halittu) na Charles Darwin. 1

A cewar Breivik, "kammalalliyar Turai" dole ta hada da dokokin zamantakewar rayuwa na Darwiniyanci. 2

A shafi na 1202 na littafinsa, Breivik yana cewa ya yarda gaba daya da masanin ilimin halittar rayuwar nan na Jami'ar Princeton, Lee Silver, dangane da sake aiwatar da nazarin jinsi (eugenics). Ya yarda da ra'ayin Silver na cewa in har ana son rage yawan jama'ar duniya zuwa kasa da rabinsu na biliyan 3.8 anan gaba to sai an aiwatar da tsauraran matakai.3

A dai wannan shafi, Breivik ya fito fili ya ayyana cewa yana goyon bayan maganar da Darwin ya yi cewa "kisan kare-dangi da kuma zabin yanayi … suna tafiya ne kafada da kafada":

 

"Koda kashe masu tasowa da matalauta sun ki amincewa da wannan "danniya" (na daina haihuwa), yanayin rayuwa zai koya musu hankali domin ba za su iya ciyar da al'ummarsu ba." 4

Breivik ya cigaba da cewa ba za a yi agaji a lokacin annobar yunwa ko ta yanayi ba:

Idan masifar yunwa ta tasamman kasashen da suka ki rungumar tsarinmu (na kayyade yawan jama'a) ba za mu tallafa musu ba ta hanyar goyon bayan lalatattun shugabanninsu ko kuma aika musu da kowane irin tallafi."

"Dole ne a dakatar da agajin abinci ga kasashe masu talauci domin shine musabbabin karuwar yawan jama'a"6

Wadannan kalmomi da Breivik ya rubuta da kansa sun bayyana karara cewa ba shi da dabi'ar kirki sakamakon karayunsa na Darwiniyanci, wanda a sakamakon haka ya kaddamar da harin ta'addanci da ya jawo mutuwar mutane da dama.

Wani misalin kuma na zagwanyewar dabi'a da aikin dabbanci da tsarin ilimin Darwiniyanci ya jawo shine Ba'ameriken nan mai kisan dauki-daidai, wato Jeffrey Dahmer, wanda ya kashe yara 17 kuma ya cinye namansu kafin a kama shi. A hirarsa ta karshe da shirin Dateline na tashar talbijin din NBC dan lokaci kafin a aiwatar da hukuncin kisa a kansa, ga abin da Dahmer ya ce:

"Idan mutum ba shi da tunanin cewa akwai wani Ubangiji da zai yi bayanin a gabansa, to me ye amfanin kokarin gyara halayyarka don ta dace da ka'dojin da aka amince? To ni haka ne tunani na. Koda yaushe ina da yakinin cewa labarin juyin halitta gaskiya ne, cewa duk mun samu ne daga digon ruwa (ta hanyar dace ko katari). Idan muka mutu, ka gane, shikenan, babu wani abu. " 7

Camfin Darwin wanda ya gurbata zuciyar mutane masu yawan gaske, ya maida mutane 'yan kisan dauki daidai da kuma tsabar haukar da ta kai har suna cin naman mutum. Wannan shine abin da addinin karyar ke haifarwa, wanda kuma ke kokarin yaudarar mutane da ra'ayin cewa babu ruwansu da Mahaliccinsu, ra'ayin da ke nuna musu cewa halittarsu ba ta da manufa, ba sa karkashin ikon kowa, haka suke kara zube ba alkibla, ra'ayin da ke daukar mutane a matsayin dabbobi kuma wanda ke neman kautar da mutane daga tunanin lahira ta hanyar cewa mutuwa ita ce karshe.

Darwiniyanci ya kasance mafi munin yaudara da annoba a karnin da ya gabata, mai kisa, danniya, ta'addanci, kisan kare-dangi, lalacewar dabia a tsawon shekaru 200 da suka gabata. DARWINIYANCI YA KASANCE MAFI MUNIN YAUDARA DA ANNOBA A KARNIN DA YA GABATA, kuma shi ne ya haddasa yakukuwan duniya da kuma akidun gurguzu da farkisanci wandanda suka shigo da kin addini, wariyar launin fata da kuma kisan kare-dangi a cikin al'ummu a wani lokaci.

Mummunan tasirin wannan bakar annoba da Darwin ya kirkiro akan al'umma ya ci gaba har zuwa wannan lokaci. Littafin kwana kwanan nan da Richard Dawkins, daya daga cikin cikakkun mabiyan Darwiniyanci a yau, ya rubuta ya kunshi bayanai wadanda suka ci karo da imani da Allah da za su iya haddasa mummunan zato da kuncin rai. Daya daga cikin fitattun misalai akan wannan shine yadda Jesse Kilgore, dalibi dan shekaru 22 a kasar Amurka, ya kashe kansa bisa tasirin littafin Dawkins wanda malaminsa ya ce ya karanta. 8

Tasirin ra'ayoyin Dawkins masu ban tsoro wadanda suka ginu akan muguwar akidar Darwiniyanci yana nan da yawa ba adadi. A gabatarwar littafinsa mai suna Unweaving the Rainbow, shi kansa Dawkins ya amince da gaskiyar lamarin:

"Wani dan kasar waje da ya buga littafi na ya bayyana cewa ya kasa barci har na tsawon kwanaki uku bayan karanta littafin, hankalinsa ya tashi dongane da abin da ya gani a matsayin sakon littafin mai bacin rai da razanarwa. Sauran mutane sun tambaye ni ta ya ya zan iya tashi da safe. Wani malami daga wata kasa mai nisa ya rubuto mini cikin fushi cewa wata daliba ta zo masa tana kuka bayan ta karanta littafin, saboda littafin ya nuna mata cewa rayuwa holoko ce marar manufa. Sai ya gargade ta da kada ta nunawa kawayenta littafin, saboda tsoron kar a gurbata musu tunani da irin wannan mummunan zato." 9

Wannan muguwar annoba, wato Darwiniyanci, baudadden addini ne wanda ke haddasa mutuwa, kisan gilla, bakin ciki, rashin imani da tausayi, ta'addanci da dabbanci sannan yana sanya muyane su ji cewa su ba komai ba ne face dabbobi wadanda suka zo duniya akan dace ko katari. Ragowar wakilan wancan addini har yanzu suna ta kokarin ganin sun kauda mutane daga imani da Allah. Shi ya sa suka dace suna adawa da koyar da raunin Darwiniyanci a makarantu, suke boye kasusuwan tarihi da ke nuna gaskiyar lamarin yin halitta, sannan ba sa yarda da cewa protein ba bisa dace ko katari yake samuwa ba da kuma cewa sama da kasusuwan tarihi miliyan 350 suke matsayin hujjar da ta rusa Darwiniyanci ba. Amma duk da wadannan matakai, mutane a karni na 21 ba sa ruduwa da karairayi. Duk kokarin cigaba da kuranta Darwiniyanci bayan an kware masa zani a matsayin yaudara ne ya ci tura.

_______________________

1- http://www.darwinthenandnow.com/2011/07/breivik-a-darwinist/?cb=09394448816310614

2- Anders Behring Breivik, A European Declaration of Independence, p.1386

3- http://www.darwinthenandnow.com/2011/07/breivik-a-darwinist/?cb=09394448816310614

4- Anders Behring Breivik, A European Declaration of Independence, p.1202

5- Anders Behring Breivik, A European Declaration of Independence, p.1202

6- Anders Behring Breivik, A European Declaration of Independence, p.1203

7- Kelly J. Coghlan, Houston Chronicle Sunday-15 February 2009

8- http://www.worldnetdaily.com/index.php?fa=PAGE.view&pageId=81459

9- Richard Dawkins, Unweaving The Rainbow New York: Houghton Mifflin Company, 1998, p. ix.

Tsarin Ilimin Darwiniyanci a Makarantu shine Babban Abin da ke Haddasa Rikici da Ta'addanci

Babu wani abu anan duniya ya faru akan dace ko katari, haka nan yake gab akin duhun da aka jefa duniya cikin a karni na 20 da 21. Ta cikin wadannan matakan wahala a tsawon tarihi, Allah ya nuna muhimmin misali ga 'yan Adam kuma har yanzu Yana son su gane shi. Akwai bukatar mutane su fahimci: Idan sun mance cewa an halicce su ne don soyayya, 'yan uwantaka, abota da kuma kyautatawa, amma idan suka zabi zama cikin rarraba da fada da juna a maimakon hadin kai da kara karfi, kuma idan suka rudu da akidu da gwagwarmayoyin karya suka yarda cewa "kisa da fada sune hanyar bukasa da cigaba," za su sami abin da suke so: fada da shiga kunci. Sannan a karshe za su gane cewa fada ba zai taba kawo bunkasa da cigaba ba, sai dai halaka.

Darwiniyanci da Reshensa na Gurguzu Sun Ginu ne Akan Manufar Fada da Rikici Heraclitus (576-480) ya bayyana musun muhawara wanda ya samo asali a tsohuwar Girka a ma'anar "muhawara" a cikin wadannan kalmomi: "…duk abubuwa sun samu ne ta hanyar rikicin abubuwa masu kishiyantar juna." Ga Heraclitus, rikici shine tushen kowane abu. Saboda haka, dole ne a sami rikici tsakanin bayani da kishiyar bayani. Idan daya bangaren za su yi nasara a kan masu kare bayani, to zai kasance ta hanyar yaki da zubar da jinni kuma za a halakar da abokin hamayya ne ta kowane hali. Dagan nan sai hadadden bayanin ya koma sabon bayani inda za a ci gaba da fada da yaki kamar yadda aka saba.

Hegel da Marx, wadanda suka zo karnoni bayansa, sun kira wannan da "rikici," idan ba yaki ba ne kai tsaye, inda kuwa ba a je ko'ina ba kafin jagororin na gurguzu sun fahimci abin a matsayin yaki da kisan kiyashi. Sun yi imani da wajibcin yaki kuma dauke shi a matsayin ka'idar akidar Markisanci. Duk yake 'yan dagajin 'yan gurguzu na wannan zamani sun yi watsi da wannan ka'ida ta yaki, gurguzu yana bukatar kwantan-bauna na rashin imani, yaki sari-ka-noke, yaki, da kuma kisan kiyashi ba tare da kakkautawa ba. Kisan kiyashin da ake yanzu a kasar Siriya, da kuma zubar da jinin da 'yan kungiyar PKK suke yi a kudancin Turkiya sun isa hujja akan wannan.

Duk Kasar da ke Fuskantar Ta'addanci a Yau Hakika Tana Fama da Gurguzu ne

Duk wata kasa da ke fama da ta'addanci kamar kasar Turkiyya, a hakika tana fada ne da gurguzu. Har yanzu gurguzu yana da ransa, koda kuma a gwamnatance ba a yarda yana nan ba; shi yake iko a wani bangare na Amurka ta Arewa, Arewacin Turai da kuma kusan gaba dayan Gabas ta Tsakiya. Sannan akwai kasashen da a gwamnatance suke karkashin mulkin gurguzu kamar da yawa daga kasashen Amurka ta Arewa, kasar Chaina da kuma Koroya ta Arewa. Wannan mulki na gurguzu ko Markisanci ya jawo ta'addanci a duniya baki daya. Wadanda suka kauda kansu ga wannan barazana ta Markisanci har yanzu suna neman hanyar magance ta'addanci ta hanyar muhawarorin talbijin da ba sa karewa. Sai dai kuma, a lokaci guda suna ci gaba da koyawa dalibansu musun muhawara a makarantunsu. Zukatan 'ya'yansu cike suke da karairayin cewa bangarori masu hamayya dole su yi fada da junansu kuma wai tarihi cike yake da wadannan rikici, da kuma cewa wai ta hanyar wadannan rikici ne za a sami bunkasa ko cigaba da kuma amfani ga al'ummu. Su kansu 'yan ta'addan an wanke kwakwalensu da wadannan karairayi. Abin mamaki, sai ga shi duka kasashen gurguzu da na jari-hujja suna koyar da irin wannan tsari na ilimi; saboda haka tunanin Markisanci ya ci gaba da bunkasa a kowace kasa da kwararan matakai na sirri.

Akwai wani abin da ya kamata yi tunaninsa: Tsarin jari-hujja ba matsala ba ne ga Markisanci. Sabanin haka, kamar yadda Marx ya fada, jari-hujja wani muhimmin mataki ne ga al'ummu na tsallakawa zuwa gurguzu. A takaice, gurguzu ya yi kwanton-bauna, yana jiran damar da zai shake tunanin mutane da al'ummu wadanda tsarin jari-hujja ya koya musu son kai, wadanda suka yi watsi da al'adunsu na addini da dabi'ar mutumtaka, masu tunanin kan abin da ya shafe su kadai. Rikicin tattalin arziki na kwanan nan ya fada hannun akidar gurguzu. A cewar mabiya Markisanci da 'yan gurguzu, komai ya kankama yanzu. Duk wanda ke son ya fahimci wannan lamari sosai yana iya yin kyakkyawan nazari akan matsalolin duniya daban daban.

Kasancewar Bangarori Masu Hamayya da Juna Ba ya Bukatar Gwabza Yaki

Dama koda yaushe akwai bangarori masu hamayya da juna. Rikici tsakanin mugum aiki da kyakkyawa ya kasance tun farkon duniya. Sai dai, za a tsaya ne a fayyace wannan rikici. Kasancewar bangarori masu hamayya da juna ba ya bukatar gwabza yaki. Masu hamayyar za su iya kalubalantar junansu ta hanyar sadarwa, muhawarorin ilimi, gabatar da hujjoji, duk cikin yanayi na soyayya da girmama juna; babu wanda za a tilastawa daukar wani ra'ayi sannan babu wanda za a kashe kawai saboda ya ki daukar ra'ayin. Zuwa yanzy babu inda yaki ya taba kawo wa wata al'umma cigaban kirki. Yakukuwa da rikicin karni na 20, fadace fadacen zamani marasa karewa, kawai suna taimakon masana'antun kera makamai ne wadanda ke samun makudan kudade wajen kera makaman da ke hallaka mutane, kasashe, ayyukan fasahar kere kere, birane da kuma gaba dayan tattalin arziki. Ba za a taba samun cigaba ko bunkasa ba da mutanen da a kullum suke tsorace. Ta ya ya za a cigaba yayin da mutane suke cikin halin yunwa, rashin isasshiyar lafiya, karancin ilimi da rashin iya aikata komai. Ta ya ya birane za su bunkasa yayin da bama bamai da jiragen yaki suke rusa gine gine da kere keren fasaharsu. Babu wata al'umma da za ta cigaba yayin da ake kashe matasanta kullum. Bama baman atom da aka jefa a biranen Hiroshima da Nagasaki ba abin da suka jawo ban da barna da aka kwashe shekaru ana ganin tasirinta. Musun tsattauran ra'ayin da Markisanci ya kawo bai haifar da cigaban da ake mafarkin faruwarsa a cikin al'ummu ba kuma hakan ba zai yiwu ba a nan gaba. Idan muka kyale wannan abu ya ci gaba, za a ga annobar da ta fi haka a duniya, inda ko'ina za zama filin zubar da jini.

Darwiniyanci shine tushen falsafar rikice rikice da yawa a duniya. Labarin juyin halitta yana ikrarin wai duk nau'in halitta sun samu ne daga kwayar halitta daya (wadda Darwiniyawan suka kasa fadar asalinta) sakamakon wasu jerin aukuwar al'amura a bisa dace ko katari. A cewarsu, fada yana daya daga cikin wadannan hanyoyin juyin halittar na mafarki. Ginshikin wannan muguwar akida, wadda ke ikrarin cewa juyin bunkasar halittu masu rai yana faruwa kadai ta hanyar fada, shine cancantarka ta kwace ka. Gabatar da wannan murdadden addini na Darwiniyawa a matsayin ka'idar kimiyya da kuma shigar da shi cikin manhajojin ilimi a ko'ina cikin duniya ya jawo gagarumar yaudara akan mutane inda kuma wadannan murdaddun ra'ayoyin Darwiniyawan suka sami kyakkyawan wajen kwasar mabiya, wanda a karshe ya haddasa hasarar miliyoyin rayuka ta hanyar yakukuwa daban daban.

Babbar Hanyar Magance Wadannan Mugayen Akidu ita ce Tumbuke Tsarin Ilimin Bangare daya da ke Yada Darwiniyanci

Ra'ayoyi masu hamayya da juna za su iya haifar da kyakkyawan abu ne kawai ta hanyar soyayya da tausayi, girmama juna, 'yancin tunani da hujjojin kimiyya.. Amma ba ta amfani da karfi ko ta'addanci ba. Lokaci ya yi da kowa zai fahimci dalilin da ke kawo wadannan annoba da suke nakasa duniya. Markisanci yana samar da hujjojin yin yaki; Al'ummun Markisanci su ne suke tsara wannan ta karkashin kasa. Babbar hanyar da za a kawo karshen wannan shine ta hanyar nuna cewa wannan mugun ra'ayi na musun tsattsauran ra'ayi hujjar kimiyya ce ta karya don kawai a halasta yaki. A gaba daya za a iya cewa musun tsattsauran ra'ayi na yanayi haukar banza ce, kuma kamar yadda yake akwai masu farautar mutane a duniya, haka nan akwai halittu masu rai da ke rayuwar ba tare da son kai ko ha'inci ba. Sassaukar hanya don cimma wannan ita ce gaggauta gyara tsarin ilimin da ke koyawa yara da matasa wannan ra'ayi na musun tsattsauran ra'ayi a fadin duniya. Wannan duniya ba filin yaki bace, gare mu, ko ga sauran halittu. Duniya za ta gyaru ne kawai ta hanyar nuna soyayya, kamar yadda Ubangiji ya saukar a dukkan saukakkun addinai. Allah yana neman soyayya daga garemu. Allah Yana son mu kasance al'umma daya, 'yan uwan juna. Allah Yana son mutane kuma Yana son su so Shi. Wannan duniya za ta canja ne idan muka bi umarnin Allah muka yi "soyayya."

Badiuzzaman Ya yi nuni ga Muhimmancin Gwagwarmayar Ilimi Akan Darwiniyanci da Zahiranci

Babban malamin musuluncin nan, Badiuzzaman, wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya cikin gwagwarmayar ilimi akan kafirfci, ya bayyana a cikin littattafansa cewa Darwiniyanci da Zahiranci su ne rike da tutar kafirci. Saboda haka sai ya ce gwagwarmayar ilimi akan wadannan akidu za ta taka babbar rawa.

Badiuzzaman ya bayyana tasirin zahiranci akan kafiran da ke kokarin kai masa hari shi da abokansa: "Na uku: Don a gurbata su da ayyukan sabo masu daukar hankali da kuma gubar falsafar zahiranci da wayewa mai bugarwa da nuna jin dadi; kuma a rusa hadin kansu; a bata shugabanninsu da karairayin cin amana; sannan a kushe hanyoyin rayuwarsu da wasu daga cikin ka'idojin kimiyya da falsafa…" (Bediuzzaman, The Treatise of Light Collection, The Rays, Thirteeth Ray)

Kamar yadda Badiuzzaman ya fada cikin hikima, kafirai sun yi nufin yaudarar masu imani da al'amuran jin dadin duniya marasa dorewa don su bata ayyukan ilimi na Badiuzzaman, kuma ta samun taimakon al'adar zahiranci ta son duniya, sun yi kokarin karya hadin kai da 'yan uwantakar masu imani sannan suka dinga batanci ga Badiuzzaman ba kakkautawa. Amma kuma ba su ci nasara ba.

Badiuzzaman yana fadin cewa Darwiniyanci da Zahiranci za su yi karfi musamman a karshen duniya kuma cewa kafirci zai yadu ta hanyar wadannan akidu guda biyu; Sai dai kuma Annabi Isa (AS) da Sayyidina Mahdi (AS) za su kawo karshen wannan masifa ta hanyar cikakkiyar gwagwarmayar ilimi. Kamar yadda Badiuzzaman ya bayyana, Sayyidina Mahdi (AS) zai gudanar da wannan aiki sosai da sosai, sannan ta hanyar ilimi zai ga bayan Darwiniyanci da zahiranci inda zai kubutar da imanin mutane.

"Na farko: Karkashin tasirin kimiyya da falsafa, da kuma yaduwar annobar 'yan zahiranci da ta 'yan dabi'ar yanayi a cikin al'umma, aikin farko (na Sayyidina Mahdi) shine ceto addini don a toshe bakin falsafa da tunanin 'yan zahiranci." (Bediuzzaman, The Treatise of Light Collection, Emirdag Addendum, p. 259)

Badiuzzaman yana cewa Darwiniyanci da Zahiranci sune matattarar dujjal, sannan kuma cewa Annabi Isa (AS) zai kaddamar da gagarumar gwagwarmayar ilimi akan wannan barna, inda zai kawar da ita: "… a karshen zamani za a tsaftace addinin Kiristanci a raba shi da camfi dangane da kafirci da zindikancin wannan zamani da ya fito daga falsafar 'yan dabi'ar yanayi, inda za a hade shi cikin Musulunci. A dai dai wannan lokaci, gungun jagororin kiristanci za su kashe gungun jagororin kafirci da takobin wahayi daga Allah; haka shi ma Annabi Isa (AS), a matsayin mai wakiltar jagororin kiristanci, zai kashe dujjal, wanda ke wakiltar jagororin kafirci, wato zai kashe akidar zindikai (zai kashe ta ne da makamin ilimi)." (Bediuzzaman, The Treatise of Light Collection, The Letters, First Letter, p. 22)

"… zai kashe [da makamin ilimi] gungun dandazon jagororin zahiranci da kafirci wanda dujjal zai kafa – domin Annabi Isa (AS) shi zai kashe dujjal da takobinsa [ta ilimi] – sannan ya rusa ra'ayi da tsarinsa na kafirci, wanda zindikanci ne." Bediuzzaman, The Treatise of Light Collection, Flashes, 5th Flash, p. 589)

Badiuzzaman Said Nursi ya bayyana karara cewa Darwiniyanci da Zahiranci su ne suka tunkude mutane daga kyawawan dabi'un addini suka ja su zuwa kafirci. Ya yi bayanin cewa Musulmai za su kaddamar da wata gagarumar gwagwarmayar ilimi akan wadannan murdaddun ra'ayoyi karkashin jagoranci Annabi Isa (AS) da Sayyidina Mahdi (AS). Da ikon Allah, wadannan bayin Allah biyu masu albarka za su kawo karshen wadannan akidu inda dabi'un Musulunci za su mamayed duniya.

Tattaunawa da Adnan Oktar

Darwiniyanci shine Sababin Ta'addanci, Amma Musulunci shine Maganin Ta'addanci

Adnan Oktar: Duk wadanda suka aiwatar da harin 11 ga Satumba mutane ne da suka yi karatu karkashin tsarin ilimin Darwiniyawa, 'yan zahiranci da zindikai, wadanda suka yi karatu a Turai kuma suke da ra'ayin son duniya na zahiranci. Katin shaidar su zai iya nuna su Musulmai ne, amma wannan ba shi da muhimmanci… An sha samun 'yan gurguzu a Falasdinu, an sha samun 'yan gurguzu a Siriya kuma an sha samun 'yan gurguzu a Iraki, amma mun godewa Allah, wadannan kasashe yanzu sun zama cikakkun masu bin addini. Amma ba shi da wani muhimmanci cewa mutumin da ya sami renon Markisanci kuma ya yi karatu karkashin 'yan tsattsauran ra'ayi, Darwiniyawa, da zahirawa sunan sa Hassan ko Mehmet. Dan zahiranci sunan sa dan zahiranci. Aikin da mabiyin Darwiniyanci ko zahiranci ya aikata sunansa aikin mabiyin Darwiniyanci ko zahiranci. Aikin mabiyan Markisanci ne. Don ba wata ma'ana a danganta shi da Musulmai. A wata ma'anar, idan muka dubi mutanen da suke aiwatar da ayyukan ta'addanci daban daban, karhse za mu ga cewa sun sami ilimin su ne karkashin Darwiniyanci. Za mu ga cewa sun yi karatu karkashin zahiranci. Shin mutumin da ke jin tsoron Allah, ya ke son Allah da dukkan zuciyarsa, wanda ya yi imani da ranar lahira kuma ya yi imani da aljanna da wuta, zai iya jefa bam akan mata da yara wadanda ba su ji ba ba su gani ba? Wace irin bajinta ce wannan? Shin mutumin da ke tsoron Allah zai sami kuzarin yin haka? Ba za su taba yin tunanin aikata wannan abu ba. Ba zai taba darsuwa a ransu ba, balle har su kai ga aikata shi. Mutanen da ke aikata wannan su ne irin mutanen da na bayyana, mutanen da ke da ilimin addini amma suke da ra'ayin Darwiniyanci da zahiranci. Akwai Markisanci-Leniyanci. Ta'addanci muhimmin mataki ne a tunanin Leniyanci. Markisanci gurguzu ne a rubuce, Leniyanci kuma gurguzu ne a aikace. Tunanin gurguzu ne a aikace. Lenin ya ce hanyar aikata gurguzu ita ce ta'addanci. Lenin ba zai taba tunanin gurguzu ba tare da ta'addanci ba. Ta'addanci muhimmin abu ne a tunanin Markisawa da Leniyawan asali. Wadannan mutane kawai suna yin abin da ya kasance muhimmi.

Duba, tsofaffin membobin jam'iyyar Ba'ath ne da kuma mutanen da suka sami horo daga gurinsu. 'yan Ba'ath na Iraki da Siriya duk sun sami karatunsu ne daga mabiya Markisanci da Leniyawa da kuma mabiyan Stalin. Musamman Iraki cike take da mabiyan Stalin. Tashin hankali yada daya daga cikin alamomin Staliniyanci. Babu inda za ka sami Staliniyanci ba tare da ka ga tashin hankali ba. Shugaban kasar Iraki, Saddam ya yi kokarin ya maida kansa wani Stalin kuma dan ga-ni-kashe-nin Stalin ne. Yana da ra'ayin Markisanci-Leniyanci. A lokuta da dama ya sha bayyana sha'awarsa akan Stalin. Kuma ayyukansa koyi ne da Staliniyanci. Kisan kiyashi, wato kashe mutane masu dimbin yawa, daya ne daga cikin hanyoyin Stalin. Saboda soyayyarsa da kuma biyayya ga Stalin, shi ma ya aikata irin abin da gwarzonsa ya aikata. An tura sojoji da jami'an Ba'ath cikin jama'a. Har yanzu suna cigaba da kashe kashen. A ce za su shiga aljanna wannan zance ne kawai. Babu wani mutum da yake da tsoron Allah kuma ya yi imani da aljanna da wuta da zai iya kisan kananan yara da sauransu. Ba zai iya kashe mutanen da ba su da laifin komai ba. Akwai ka'dar yaki a Musulunci. An bayyana wannan a cikin Alkur'ani. Tana nan cikin sunnar Annabinmu (SAW). Ana gwabza yaki ne don tsare kai sannan kuma an hana taba mata da yara. An hana… Akan ayyana yaki ne akan kasa. Dole ne yaki ya zama bisa ka'idar doka, gwagwarmaya akan tsararren kundin doka. Yarjejeniyoyin zaman lafiya da mutum ya kulla da wasu kasashe ba a karya su; abu ne da ba zai karbu ba ga mutum uku ko hudu su ayyana yaki. Kuma musamman hari akan yara da makamantansu sam sam ba abu ne da zai karbu ba. Wajibi ne a kyale su. Za a iya yada musulunci ta cikin zukatan mutane tare da al'ada, ilimi, soyayya da kuma ayyukan fasaha. Ba ta hanyar fushi ba. Ba ta zubar da jini ba. Annabinmu (SAW) ya kan tafi zuwa kasuwar Ukaz, inda mutane ke zagin wannan bawan Allah mai kyawun hali.Su kan jefa kaya a kan hanyarsa don ya taka. Sun jefa mahaifar rakumi akansa. Amma sai ya ci gaba da wa'azi kawai. Ya yi musu bayanin Musulunci da Alkur'ani. Ya yi hakan ne cikin soyayya da rashin gajiyawa na tsawon shekaru. A karshe dai, kamar yadda ka sani, ya kasa jure gallazawarsu inda ya yi hijira. Ya ci gaba da wa'azi a wuraren da ya ziyarta yayin hijirar. Duk yakukuwan Annabi (SAW) yakukuwa ne na kariya.Yakukuwa ne na kare kai. Bai taba zuwa wani gari ya kwace garin da karfin makamai ba. Koda yaushe yakin kare kai yake yi. (Azernews, 23 gs Oktoba 2008)

Cikakken Zamani na Wayewa da Cigaba Zai Bayyana Yayin da Mutane Suka Rungumi Dabi'un Musulunci

Adnan Oktar: Duniyar Kiristanci tana da Fafaroma, amma duniyar Musulunci ba ta da jagora. Dole ne duniyar Musulunci ta Turkiyya ta kasance tana da jagora kuma mai hadin kai. Yayin da aka kafa wannan hadaddiyar daula, yayin da duniyar mulunci ta Turkiyya ta kasance a dunkule, nan da nan za a ga wadannan kyawawan dabi'u , nan take, kuma za su yadu ko'ina. Babu mai yin watsi da su. Idan addinin ya ci gaba da zama a hannun jahilai ko masu raunin imani, na mutanen da ba sa karanta littattafai balle su fahimci duniya, to kuwa za a iya samun ta'addanci, rushewar doka da oda, kisan kai, talauci, gaba da kimiyya da kuma komai. Sai dai Musulunci addini da ya zama wajibi mutane su hada kai a cikinsa. Yayin da aka kafa Hadaddiyar Daular Musulunci ta Turkiyya, yayin da aka sami jagorancin addini, wannan jagoranci na addinin zai kauda wadannan matsaloli lokaci guda. Za a maye gurbin wadannan da soyayya, kauna, tausayi, abota da 'yan uwantaka. Za a sami cikakkiyar al'umma mai wayewa da cigaba. Shi ya sa na ke son ganin an kafa Daular Musulunci ta Turkiyya ba da bata lokaci ba. (Associated Press ta Pakistan, 6 ga Satumba, 2008)

Shi ne Wanda ke saukar da ayoyi bayyanannu ga BawanSa, domin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske. (Alkur'ani, sura ta 57, aya ta 9)

8 / total 10
You can read Harun Yahya's book Musulunci Ya La'anci Ta'addanci online, share it on social networks such as Facebook and Twitter, download it to your computer, use it in your homework and theses, and publish, copy or reproduce it on your own web sites or blogs without paying any copyright fee, so long as you acknowledge this site as the reference.
Bayani akan shafin | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to author “Mr. Adnan Oktar”.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top